Sojojin MDD hudu sun mutu a hannun Anti-Balaka | Labarai | DW | 10.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin MDD hudu sun mutu a hannun Anti-Balaka

Sakatare janar na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda aka hallaka sojojij kiyaye zaman lafiya hudu wasu da dama suka jikkata

Antonio Guterres a wata sanawar da ya fitar, yace harin an kai shi ne a kan kwambar dakarun kiyayen zaman lafiya inda nan take soja hudu suka mutu wasu kimanin 10 aka kai su babban asibiti a Bangui babban birnin Kasar. Sanarwar ta kara da cewa kawo yanzu akwai soja guda wanda ya bace bayan harin. Ana dai tuhumar 'yan kungiyar anti-Balaka da ke zama mayakan kiristoci da kai farmakin. Lamarin ya farune a kan iyakar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango