Sojojin Mali sun karɓi iko da garin Ménaka. | Labarai | DW | 12.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Mali sun karɓi iko da garin Ménaka.

Haɗin gwiwar sojojijn Mali da na Faransa sun shiga garin na Ménaka da ke a yankin arewaci kan iyaka da Niger ba tare da yin wani faɗa ba.

Wani babban habsan soji na Mali kanal Alaji Ag Agamu ya shaida cewar su ne da sojojin Faransa ke riƙe da garin tun sao'i 48 da suka wucce.Ya kuma ce kafin su isa a garin, mayaƙan ƙungiyar yan tawaye na MNLA sun arce, sannan kuma ya ce sun kama wasu dakarun ƙungiyar guda uku.

Tun a ranar biyar ga watan Febrairu bradan na ƙungiyar ta MNLA suke a garin na Ménaka wanda da farko ke cikin hannu masu kishin addini kafin su ficce.Wannan shi ne gari na kusan biyar da sojojin Faransa da na Mali suka karɓe daga hannu yan tawayen.Yanzu haka sojojin ƙasashen sun ƙara ƙarfafa matakan tsaro ta hanyar gudanar da bincike a kan jama'a masu yin shigi da fuci.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal