1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Mali na kokarin kwaco Konna

January 11, 2013

Rundunar sojojin Mali ta afka wa 'yan Ansar Dine da yaki a Konna da nufin kwaco birnin daga hannunsu. Sai duk da harin da suka kai ta sama hakar su ba ta cimma ruwa ba.

https://p.dw.com/p/17I0d
Hoto: dapd

Rundunar sojojin Mali ta kai farmaki birnin Konna da ke tsakiyar kasar da nufin kwaco garin da masu kaifin kishin Islama suka mayar karkashin ikonsu tun jiya alhamis. Wata sahihiyar majiyar soje da kuma mazauna birnin sun baiyana cewa jiragen gwamnati masu saukar angulu sun kai wa 'yan Ansar Dine hare haren boma bomai. Sai dai kuma kakakin ita kungiyar da arewacin Mali ke hannunta ta ce har ya zuwa yanzu birnin Konna na hannunta. Da ma dai wannan birnin shi ne shinge ko iyaka tsakanin bangaren da ke karkashin ikon Ansar Dine da kuma bangaren Mali da ke karkashin gwamnati.

Shugaba Faransa François Hollande ya ce kasarsa a shirye ta ke ta taimawa Mali fatattakar masu kaifin kishin addinin idan suka ci gaba da kwace wasu biranen. Mambobin 15 da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kunsa sun bukaci a hanzarta turawa da sojojin kasa da kasa Mali domin ja wa masu kaifin kishin addinin musulunci birki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman