1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali sabon salo na juyin mulki

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2021

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman kan rikicin Mali, sa'o'i bayan da sojojin suka kwace mulki daga gwamnatin rikon kwarya.  

https://p.dw.com/p/3txJx
Mali Bamako Feierlichkeiten 60 Jahre Unabhängigkeit
Hoto: Michele Cattani/AFP

A wata sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Talata, Kanal Assimi Goïta jagoran juyin mulkin na Mali, ya bayyana cewa shugaban gwamnatin rikon kwarya Bah Ndaw da firaministansa Moctar Ouane, sun sabawa tsarin tafiyar da mulkin gwamnatin kasar ta wucin gadi, kwana daya bayan sun aiwatar da wasu muhimman sauye-sauye a majalisar ministoci.

Tuni manzo na musamman na kungiyar ECOWAS kan rikicin Mali kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sauka a birnin Bamako don tattauna rikicin da ya sake barkewa, a yayin da a share daya kasashen Ecowas da Faransa ke ci gaba da yi wa sojan matsin lamba, tare da barazanar daukar mataki na ladabtarwa.

Ana sa ran a wannan Laraba tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan, zai gana da Bah Ndaw shugaban kasar ta Mali da soja suka kama da firaminstansa Moctar Ouane a barikin Kati da ke wajen birnin Bamako.