1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana neman jirgin da ya bata da mataimakin shugaban Malawi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 11, 2024

Mr Chakwera ya ce Amurka da Burtaniya da Norway da kuma Isra'ila sun yi tayin bada agajin neman jirgin

https://p.dw.com/p/4gtLG
Hoto: AMOS GUMULIRA/AFP

Shugaban Malawi Lazarus Chakwera, ya ce sojojin kasar na ci gaba aikin laluben jirgin saman da ya yi batan dabo, dauke da mataimakinsa Saulos Chilima, da kuma Shanil Dzimbiri, tsohuwar matar tsohon shugaban kasar Bakili Muluzi.

Karin bayani:Limaman Kirista na ci gaba da saba wa yin tabarruki ga auren jinsi

Mr Chakwera ya ce hakika suna cikin tashin hankali, amma dai sojoji sun dukufa cikin dazuka da tsaunuka don neman jirgin, kuma Amurka da Burtaniya da Norway da kuma Isra'ila sun yi tayin bada nasu agajin, wajen fafutukar neman jirgin a duk inda ya ke.

Karin bayani:Malawi: An kama Saulos Chilima

Jirgin dai ya tashi ne da karfe 9:17 na safiyar Litinin a filin jirgin saman birnin Lilongwe, amma daga nan ne sadarwa ta katse tsakaninsa da jami'an da ke bibiyarsa.