Sojojin Kamaru sun kashe ′yan Boko Haram sama da 100 | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Kamaru sun kashe 'yan Boko Haram sama da 100

Mahukunta ƙasar sun ce an kashe mayaƙan Boko Haram ɗin a garin Fotokol da ke a yankin arewa mai nisa na ƙasar kan iyaka da Najeriya.

A cewar mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ta Kamaru Issa Tchiroma Bakary da ya ke jawabi ta kafar gidan rediyo na ƙasar. Ya ce dakarun sojin na Kamaru sun yi babbar illa ga Ƙungiyar ta Boko Haram a fafatawar da suka yi da su a ranar Asabar a yanki arewa mai nisa na Kamarun.

Yazuwa yanzu dai babu wata kafa da ta tabbatar da gaskiyya wannan labari, kuma hukumomin na Kamaru sun rufe ɗaukacin makarantun da ke a yankin na arewa mai nisa saboda dalilan tsaro.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu