1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Ethiopiya sun kwace wani yanki

Zainab Mohammed Abubakar
December 1, 2021

Sojojin Ethiopiya da ke samun goyon bayan dakarun yankin, sun sanar da sake kwace wani yanki daga wajen mayakan tawaye na Tigray a cewar sanarwar ofishin framinista.

https://p.dw.com/p/43hUA
Äthiopien | Premierminister nimmt an Offensive gegen Rebellentruppen Teil
Hoto: Ethiopian Prime Minister's Office//AA/picture alliance

Sanarwar na zuwa ne bayan nasarar da dakarun gwamnatin suka sanar da samu a yankin Amhara a karshen mako, na sake kwace Chifra da ke gundumar Afar, bayan da Framinista Abiy Ahmed ya bar babban birnin kasar Addis Ababa, domin shiga yaki kai tsaye a makon da ya gabata.

Nasarar mayakan gwamnatin dai, koma baya ne ga mayakan na Tigray da ke fatan isa birnin Addis Ababa da yaki ta cikin garin Amhara a kudanci, a ci gaba da yakin shekara guda na wannan kasa da yayi sanadiyyar dubban rayukan mutane tare da tilasta wasu miliyoyi kauracewa matsugunnensu.