Sojojin Amirka sun aikata laifin yaki a Afghanistan
October 6, 2015Shugabar ta Medecin sans Frontieres ta kara da cewa, labarin da 'yan kasar Afghanistan suka bayar na cewa 'yan Taliban na fake wa da wannan babban asibiti suna kai hare-hare, ya nunar cewa harin da aka kai ba bisa kuskure ne ba. A wannan Talatar ce kuma Janar John Campbell, babban kwamandan sojojin kasar ta Amirka da kuma na kungiyar tsaro ta NATO ya sanar cewa sojojinsu sun kai hari a ranar Asabar da ta gabata, ga wani babban asibiti na Medecin sans Frontieres da ke birnin Kunduz bisa kuskure, harin da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 22.
Tuni dai ma'akatar shari'a ta kasar Amirka ta sanar da aniyarta ta gudanar da bincike kan lamarin, yayin daga nashi bangare shugaban kasar Barack Obama ya ce ya kyautu a yi taka tsan-tsan na ganin irin haka bai kara faruwa ba a nan gaba.