Sojoji sun hallaka kwamandan Boko Haram
August 14, 2013Rundunar tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya da aka sani da JTF, ta sanar da cewa ta samu nasarar hallaka Momodu Bama da ake wa laƙabi da Abu Saad, wanda babban kwamandan ƙungiyar Boko Haram wanda ke zama na biyu a karfin iko, bayan jagoran ƙungiyar Imam Abubakar Shekau. A wata sanarwar da kakakin rundunar Laftanar kanar Sagir Musa ya aikewa manema labarai, ya ce rundunar ta samu nasarar hallaka Momodu Bama a wani gumurzu da aka yi, yayinda jami'an tsaron ke kokarin magance wani hari da ‘yan ƙungiyar gwagwarmayar suka nemi kai wa a garin Bama a farkon watan nan. A cewar wakilinmu Amin Sulaiman Muhammad, Momodu Bama da ake yi wa laƙabi da Abu Saad yana cikin waɗanda kasar Amirka ta sanya makuɗan kuɗaɗe akan su, kuma babban na hannun daman jagoran kungiyar ne. Babu dai wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin jami'an tsaron.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Saleh Umar Saleh