Sojoji na ci gaba da hare-hare a biranen kasar Cote d′Ivoir | Labarai | DW | 15.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji na ci gaba da hare-hare a biranen kasar Cote d'Ivoir

Rahotanni daga birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoir na cewa, ana ci gaban da fuskantar borin sojoji a birnin Bouake da ke arewacin kasar, da kuma Abidjan babban birnin kasar, inda sojojin masu bore suka kafa shingaye.

Elfenbeinküste Soldatenmeuterei (Getty Images/AFP/I. Sanogo)

Sojoji masu bore a kasar Cote d'Ivoir

Wani mai magana da yawun sojojin da ke bori a birnin Abidjan ya sanar a wannan Litinin din cewa, tattare hanyoyi da suka yi, da kuma harbe-harben da suke yi ba juyin mulki ba ne, illa kawai nuna buktar su ta a biya su kudadansu kamar yadda shugaban kasar Alassane Ouattara ya rattaba hannun cewa zai biya su.

A ranar Alhamis ce dai da ta gabata wani mai magana da yawun sojojin da suka yi bori a kasar ya nemi gafara a gaban Shugaban kasar Alassane Ouattara dangane kan borin da suka yi a baya, inda kuma ya sanar cewa sun yi watsi da dukannin bukatunsu na neman a biya su wasu kudaden na alawus, sai dai kuma ga dukkan alamu wannan mataki bai yi wa saurau sojojin dadi ba.