1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban da sojin kabul sun koma gidan jiya

Mouhamadou Awal Balarabe
May 16, 2021

Fada ya sake kaurewa tsakanin 'yan Taliban da dakarun Afhganistan bayan tsagaita bude wuta na kwanaki uku da suka yi a karamar sallah, inda suka fara ba wa hamata isa a lardin Helmand.

https://p.dw.com/p/3tSmp
Konflikt in Afghanistan
Hoto: Rahmat Gul/AP Photo/picture alliance

Bayan mutunta shirin tsagaita bude wuta na kwanaki uku a yayin bikin Eid-el-Fitr na Musulmi a Afghanistan, mayakan kungiyar Taliban da ke tsananin kishin Islama da sojojin gwamnati sun sake komawa fagen yaki tsakaninsu. Wani kakakin rundunar sojojin Afghanistan ya bayyana cewa wani sabon rikici ya barke tsakannin sassa biyu da ke gaba da juna a kudancin lardin Helmand da ke kudancin kasar. Babu wani karin haske da aka bayar dangane da wadanda suka rigamu gidan gaskiya ko suka ji rauni yayin wannan fada.

Sai dai wannan tashin hankali ya zo a daidai lokacin da  kungiyar masu da'awar jihadi ta IS ta dauki alhakin kai hari a wani masallaci da ke kusa da Kabul babban birnin kasar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 a ranar Jumma'a. Tashin hankali ya karu matuka a Afghanistan tun bayan da sojojin kasa da kasa musamman ma na Amirka suka fara janyewa daga kasar a farkon watan Mayu.