Soji bakwai sun mutu a Arewacin Mali | Labarai | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soji bakwai sun mutu a Arewacin Mali

Sojoji bakwai da suka hada da hudu na rundunar Munisca da uku na gwamnatin Mali sun halaka a cikin tagwayen hare-haren ta'addanci da aka kai a wannan Jumma'a a Arewacin kasar.

Rahotanni daga kasar Mali na cewa sojoji bakwai suka halaka a cikin tagwayen hare-haren ta'addanci da aka kai a wannan Jumma'a a Arewacin kasar.

Hari na farko a kai shi ne da sanhin safiyar wannan Jumma'a a barikin sojojin rundunar zaman lafiya ta MDD a Mali wato Munisma da ke a birnin Kidal na Arewacin kasar inda sojojin rundunar ta Munisma hudu suka kwanta dama ayayin da wasu kimanin 30 suka ji rauni.

Daura da wannan wasu sojojin gwamnatin Mali uku sun halaka a yayin da wasu biyu suka ji rauni a cikin wani harin kontar bauna da aka kai masu a yankin Tombouctou na Arewa maso Yammacin kasar.

Tuni dai Kungiyar Aqmi ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare wadanda suka wakanana a daidai lokacin da sabon jagoran rundunar ta Munisma Mahamat Saleh Annadif ya soma ziyararsa ta farko a farkon wannan mako a yankin Arewacin kasar ta Mali.