Snowden na neman mafaka a nahiyar Turai | Labarai | DW | 02.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Snowden na neman mafaka a nahiyar Turai

Ana ci gaba da samun takaddama tsakanin Amirka da nahiyar Turai biyo bayan tonon silili da tsohon jami'in Hukumar Tsaron Amirka ya yi na tatsar bayanai.

Tsohon ma'aikaci a Hukumar Tsaron Amirka Edward Snowden da a yanzu haka Amirkan ke nema ruwa a jallo, ya nemi mafakar siyasa a Rasha da wasu kasashe 21 da suka hadar da kasashen kungiyar Tarayyar Turai.

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen na kungiyar EU da Snowden ya mika bukatar su bashi mafakar siyasa ta hannun kamfanin Wikileaks, sun hadar da Norway da Jamus da Italiya da Faransa da Netherlands da Poland da Spain, inda kamfanin na Wikileaks ya kara da cewa ya na tunanin nema wa Snowden mafaka a baki dayan kasashen dake cikin kungiyar ta EU.

Snowden ya nemi mafakar siyasa a Rasha ne, biyo bayan haske da shugaban kasar Vladimir Putin ya bashi na cewa Rashan za ta iya bashi mafakar siyasa in har ya dakatar da ci gaba da yin tonon silili ga Hukumar Leken Asirin Amirka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Muhammad Abubakar