1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Senegal ya gawurta

March 14, 2023

Shugaba Macky Sall na Senegal na takun saka da jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da ke zargin shugaban da kafar ungula ga tsarin dimukaradiyyar kasar.

https://p.dw.com/p/4OeBg
Macky Sall | Shugaban kasar Senegal
Shugaba Macky Sall na SenegalHoto: JEROEN JUMELET/ANP/picture alliance

Takun saka na dada yin kamari tsakanin Shugaba Macky Sall na Senegal da jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin fararen hula da ke zargin shugaban da yi wa dimukuradiyyar kasar karan tsaye tun bayan da ya nemi tsayawa takara a karo na uku. A wannan Talata dai ana sa ran masu adawa da aniyar shugaban ta tsaya wa takara, za su yi jerin gwano a birnin Dakar domin kalubalantar matakin nasa.

Shekaru kusan biyu ke nan da kura ke tashi a fagen siyasar Senegal, kuma yayin da zaben kasar wanda za a gudanar a shekarar 2024 ke karatowa. Takun saka tsakanin Shugaba Macky Sall da abokan hamayarsa da kuma kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam, na kara daukar dumi. Kame-kamen 'yan jarida da hana izinin yin zanga-zanga da kuma yi wa fannin shari'a karan tsaye, na zaman kadan daga cikin ababen da ake zargin Shugaba Macky Sall da yi domin tsaya wa takara a karo na uku. Wannan lamari ya saka tsananin damuwa ga matasa kan makomar siyasar kasar, wacce a baya ake misali da ita a yammacin Afirka.

Senegal l Zanga-zangar 'yan adawa a birnin Dakar
Zanga-zangar 'yan adawa a kasar SenegalHoto: Zohra Bensemra/REUTERS

To sai dai ga Souleymane Gueye memba a jam'iyyar Front pour une Revolution anti-imperialiste populaire et Panafricaine, wacce ke adawa da Shugaba Sall tana ganin babban tushen rikicin siyasar kasar shi ne dagewa da shugaban mai barin gado ya yi na tsayawa takara a zaben da ke tafe a shekara mai zuwa. Ko baya ga wannan shawara ta hawa kan taburin tattawa da gudumowar dattijan kasar, Youssoupha Diaw na ganin cewa malaman addini ma ka iya tsoma bakinsu domin kashe wutar rikicin.

Daga wannan Talata dai jam'iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula a Senegal, sun sha alwashin gudanar da jerin zanga-zanga a birnin Dakar fadar gwamnatin kasar domin yi wa shugaban mai barin gado Macky Sall matsin lamba na janye aniyarsa ta tsayawa takara a zaben da ke tafe da kuma kalubalantar kame-kamen 'yan siyasa da 'yan jarida da ya kaddamar kan masu neman kawo masa cikas a burin da ya saka a gaba.