1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Siyasar Belarus: Lukashenko ya ce zai tsaya takara

February 25, 2024

Shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko da ke sharafinsa a karagar mulkin kasar tun a 1994, ya ce zai sake tsaya wa takara a zaben 2025, kasancewar babu shugaban da ke kaunar al'ummarsa da zai yi ''watsi da su''.

https://p.dw.com/p/4cs4i
Shugaban Belarus Alexander Lukaschenko a birnin Minsk
Shugaban Belarus Alexander Lukaschenko a birnin MinskHoto: ALEXANDER NEMENOV/AFP/Getty Images

Alexander Lukashenko 'dan shekara 69, shi ne ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai jim kada da kammala kada kuri'a a zaben 'yan majalisa da na shugabannin kananan hukumomi irinsa na farko da aka gudanar a kasar tun a 2020, wanda ya bai wa Lukashenko damar sake hawa shugabancin kasar a karo na shida.

Karin bayani:Rasha da Belarus sun soma atisayen soja na hadin gwiwa

Zaben Lukashenko a 2020 din dai, ya haifar da rudani a fadin kasar bayan da Hukumar Zaben  Belarus din ta sanar da nasarar sa.Jagorar adawar kasar da ke gudun hijra a kasashen waje Svetlana Tsikhanouskaya, ta ce sam babu dimukuradiyya a zaben.

Karin bayani:Rasha: Girke makamai a Belarus