Siriya na cikin halin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 05.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya na cikin halin tsaka mai wuya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa sama da mutane miliyan tara na buƙatar agajin gaggawa a Siriya wato kimanin kishi 40 daga cikin ɗari na al'umar ƙasar.

Babbar jami'ar Hukumar MDD da ke kula da ayyukan jin ƙai Valerie Amos ta ce al'amura sun ƙara taɓarɓarewa a ƙasar Syriya a cikin shekaru biyu da rabi na baya-bayannan. Mutane miliyan shida ne yaƙin da aka kwashe kusan shekaru uku ana yi, ya tilastawa barin gidajensu. Yayin da wasu aƙalla dubu 100 suka rasa rayukansu tun lokacin da aka fara tashin hankali a shekarar 2011.

Yau talata (05.11.2013) aka shirya manzon musammum na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma kasashen Larabawa a kan Siriyar Lakhdar Brahimi da wakilan ƙungiyar ƙasashen larabawa da na sauran ƙasashen za su gana a Jeniva domin tsayar da ranar da za a yi taron Jeniva na biyu a kan Siriyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe