Silvio Berlusconi zai komawa fagen siyasa | Labarai | DW | 09.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Silvio Berlusconi zai komawa fagen siyasa

Wannan ba shi ne karo na farko ba da tsohon shugaban gwamnatin ƙasar Italiya ke bayana janyewa daga fagen siyasa amma kuma ya cenza shawara.

default

Silvio Berlusconi

A wani abun da ke kama na bazata,wata sanarwa daga jam'iyar tsohon Faraministan Italiya ,Silvio Berlusconi,ta bayana cewar a zaɓɓuɓukan majalisar dokokin da za a shirya nan bada jamawa ba,Berlusconin za sake aza takararsa domin ceto abun da ya rage ga kasar ta Italiya da ke cikin matsalar tattalin arziki a cewar sanarwar. Waɗannan bayanan na zuwa ne jim kaɗan bayan da shugaban gwamnatin ƙasar Mario Monti ya bayanawa shugaban ƙasar Giorgio Napolitano bukatarsa ta aje madafun ikon kasar nan gaba kadan. Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da Berlusconin dan shekaru 76 da haifuwa, ke yin amai yana lashewa akan kakkaɓe hannuwansa daga siyasa idan aka yi la'akari da wannan shi ne karo na 6 yana bayana hakan. To saidai sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake jiran sa a kotu akan tarin shari'o'i da dama da keda nasaba da cin hanci da rashuwwa. Silvio Berlusconi dai shi ne shugaba na farko a duniya da ya je kotu so daya daya har so 23.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi