Siliman tafi da gidanka a Afrika ta Kudu | Zamantakewa | DW | 22.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Siliman tafi da gidanka a Afrika ta Kudu

Wani matashi mai suna Calvin Phaala ne ya fito da fasahar domin bawa mutanen karkara da ba su da akwaitin talabijin damar kallon wasannin kwaikwayo a saukake.

Calvin Phaala wani matashi mai kimanin shekaru 24 da haihuwa wanda ya fito da wannan fasaha inda a kowane dare na Allah yake amfani da majigin nasa wanda yake haskawa a bisa wani kyalle da yake bugawa a jikin gini a madadin akwaitin talabijin. Ta hanyar wannan majigi ya ke bawa al'ummar kauyensu na Garinsa damar kallon wasanni kwaikwayo musamman irin na cikin gida. Kuma tarin jama'a ne ke taruruwa a kowane dare domin kashe kwarkwatar idanunsu.

Kwalliya na biyan kudin sabuni a sana'ar

Wannan sana'a dai ta sa Calvin zama fitaccen gwarzo a fagen nishadantarwa a garinSiyabuswa, inda ya shafe watanni biyu ya na wannan sana'a kuma da alamu kwalliya na biyan kudin sabulu tunda akalla bai gaza samun sama da dala takwas a duk mako. Sai dai Calvin ya ce wannan sana'a tasa na fuskantar kalubale.

"Babban kalubale gareni dai shi ne masu satar fasaha, mutane na samun sabbin fina-finai, amma na jabu ne. Ni kuma ba zan iya nuna fina-finan jabu ga al'umma ba."

Al'umma na yabawa da fasahar Calvin

A wani kokari na neman bunkasa wannan sana'a tasa lokaci zuwa lokaci Calvin na bin gida gida wajen wayar wa al'ummar kai dangane da mahimmancin gidan kallon fina-finai ga zamantakewarsu ta duniya. Nombulelo Trudy Qwasho, daliba ce da ke bayyana gamsuwarta kan himmar da Calvin ke da ita wajen cimma burinsa.

Kongo Fußball WM 2010


"Babu gidajen kallo, ko wuraren da za'a kalli fina-finai, balle ma a ce irin wuraren debe kewa tare da abokan arziki."

Wannan aiki na fina-finai dai, ya bunkasa kasuwancin Calvin matuka. Kuma har ya soma tanadin wata sabuwar sana'ar ta saida abinci da mahaifiyarsa a duk lokacin da ake nuna fina-finan da ke basu damar samun wasu kudaden shiga.

Sauti da bidiyo akan labarin