Venezuela: Jawabin shugabar kasa na farko
January 15, 2026
Jawabin shugabar rikon kwarya ta Venezuela Delcy Rodríguez na zuwa ne, kwana guda bayan da ta sanar da cewa gwamnatinta za ta ci gaba da sakin fursinonin siyasa da aka tsare a karkashin jagorancin Nicolás Maduro da ta gada, a wani abu da ta bayyana da sabon takun siyasa. Ana dai sa ran za ta sanar da sabuwar mahangar gwamnatinta da ma sauye-sauye a kamfanin man fetur na kasar da Shugaba Donald Trump ya ce zai farfado da shi.
Shugaba Rodríguez dai na cikin tsaka mai wuya, inda take fuskantar matsin lamba daga Amurka da kuma gwamnatin da ke goyon bayan hambararren shugaban kasar Maduro da Amurka ta sauke makonni biyun da suka gabata. A wani labarin kuma, sojojin Amurkan sun sake kwace wata tankar dakon man fetur a Tekun Caribbean, wadda gwamnatin Shugaba Trump ta ce tana da alaka da Venezuela.