Shugabannin kudancin Afrika zasu gana da Mugabe | Labarai | DW | 29.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin kudancin Afrika zasu gana da Mugabe

Shugabannin kasashen kudancin Afrika sun shirya ganawa da shugaba Robert Mugabe a yau alhamis domin tattauna halinda ake ciki na tabarbarewar siyasa da tattalin arzikin kasar ta Zimbabwe.

Wannan ganawa dai ta biyo wani sabon samame ne da yan sanda suka kai kann yan adawa,wadda ta kai ga sake tsare shugaban jamiyar adawa ta MDC Morgan Tsvangarai.

Kodayake jamian tsaro na kasar sun karyata wannan batu,amma sunce sun tsare yan adawa kusan 10 bisa zargin cewa suna da hannu cikin wasu hare hare da aka kai da bam din fetur.

A halinda ake ciki kuma kasar Jamus dake rike da shugabancin kungiyar taraiyar turai tayi kira ga gwamnatin kasar ta Zimbawe da ta mutunta doka da oda na kasar.

Makonni uku da suka shige ne dai Tsvangarai da wasu yan adawa suka sha kashi a hannun yan sanda.