1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila da Falasdinawa sun yi ganawar koli

Abdullahi Tanko Bala
August 30, 2021

Ministan tsaron Israila Benny Gantz ya gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a karon farko cikin shekaru da dama inda suka tattauna karfafa huldar tattalin arziki da 'yancin walwala.

https://p.dw.com/p/3zhm5
AFP Bildkombo Mahmud Abbas  Benny Gantz
Hoto: Thaer Ghanim/Menahem Kahana/AFP

Bayan dangantaka ta kusa lalacewa baki daya a tsakanin Israila da Falasdinawa shugabannin yankunan biyu sun gana kwanaki biyu bayan da shugaban Amirka Joe Biden ya bukaci Israila ta yi kokarin taimakawa wajen inganta rayuwar Falasdinawa.

Musamman ministan tsaron Israila Benny Gantz da shugaba Mahmud Abbas sun tattauna bunkasa tattalin arzikin yankin gabar yamma da Israila ta mamaye.

Jami'an Falasdinawa sun ce Abbas ya bukaci Gantz ya dakatar da farmakin soji a yankin gabar yamma tare da bada dama ga dangin Falasdinawa su hadu da iyalansu da ke cikin Israila sannan a bada karin dama ga Falasdinawa su yi aiki a cikin Israila.

Rahotanni dai sun baiyana cewa shugaban Amirka Joe Biden na goyon bayan shirin masalaha na kasashe biyu da za su zauna daura da juna tsakanin Falasinawa da Israila.

Biden ya baiyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Firaministan Israila Naftali Bennet a fadar White House a makon da ya gabata.

Sai dai Hamas dai ta yi fatali da wannan ganawa.