1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar ECOWAS ta isa Mali

July 23, 2020

Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar Mali na cewa jiragen shugabannin Afirka ta Yamman nan guda biyar sun fara sauka a kasar.

https://p.dw.com/p/3foqZ
Krise in Mali | ECOWAS | Alassane Ouattara und Boubou Cissé
Hoto: Présidence du Mali

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce tuni Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast da Macky Sall na Senagal suka isa Malin. Daga baya kuma ana saran saukar jiragen shugabannin Najeriya da Nijar da kuma Ghana. 

Ana sa rai dai shugabannin  za su sasanta rikicin siyasar da ya yi wa kasar Mali daurin demon-minti bayan da 'yan adawa suka ja ''daga'' suka kafe-kai-da-fata sai Shugaba IBK ya sauka daga mulki, yayin da shi kuma yake neman yadda zai iya tsira da rigar mutumci.