Shugabannin Deutsche Bank sun yi murabus | Labarai | DW | 07.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugabannin Deutsche Bank sun yi murabus

A wani mataki na yadda kwallon mangwaro su futa da kuda, Deutsche Bank ya sanar da murabus din shugabanninsa a wannan Lahadin.

Shugabannin bankin guda biyu dai sun hada da Anshu Jain, dan shekaru 52 da haihuwa da ke dan asalin kasar Indiya kuma yana dan kasar Burtaniya, da kuma Jürgen Fitschen, dan kasar Jamus mai shekaru 66 da haihuwa, na jagorancin bankin ne tun daga watan Mayu na 2012 inda kuma tun yau da 'yan watanni, suke fuskantar suka sosai abun da ya tilasta musu yin wannan murabus na bazata ganin cewa wa'adin shugabancin nasu na kawo karshe ne a watan Maris na 2017.

Yanzu dai kallo ya koma ga John Cryan dan shekaru 54 da haihuwa kuma dan kasar Burtaniya, da ke a matsayin memba a majalisar sa ido ta bankin na Deutsche Bank, wanda ake ganin shi ne zai taka rawar gani wajan dawo da martabar wannan banki.