Shugabannin APC sun dira a jihar Rivers | Siyasa | DW | 05.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugabannin APC sun dira a jihar Rivers

Yayinda jam'iyyar APC ke ci gaba da zawarcin bijirarrun jam'iyyar PDP, sun isa Fatakol, inda su ka gana da gwamna Rotimi Amaechi a yunkurin jawo shi cikinsu

Babbar jamiyyar adawa ta APC a Najeriya ta gayyataci bangaren sabuwar jam'iyyar PDP a Jihar Rivers, don hadewa a yi tafiya daya domin kafa sabuwar Gwamnati a Najeriya. Sai dai daga furuce-furuce da aka yi a gurin wannan taro, da alama adawar siyasa a Najeriya ta na dada zafafa.

Bayan dai bude taro da kade-kade da raye-raye, da su ka gudana a cikin harabar gidan gwamnatin Jihar ta Rivers, inda dubban magoya baya suka halarta. Akwai jawabai da gaggan yan jamiyyar ta APC suka gabatar. Daga masu jawaban kuwa akwai Bola Ahmad Tinubu da ya bayyana takaicin dalilan da ya sa taron bai gudana jiya ba, kamar yadda aka tsara sai yau Talata.

Muhammadu Buhari from the opposition party ANPP (All Nigeria People's Party) acknowledges support after voting in Daura, Nigeria, Saturday, April. 19, 2003. President Olusegun Obasanjo seeks a second term in elections Saturday that pose the stiffest test for Nigeria's young democracy since his election four years ago ended 15 years of military rule. (AP Photo/Schalk Van Zuydam)

Janar Muhammadu Buhari

Ya ce "bama son tashin hankali ko yamutsi, so muke mu zo jihar Rivers cikin kwanciyar hankali, don mu sadu da kowa a nan, bisa neman hadin kanku a tafiyar siyasa tare. Shi ya sa muka ce a samu nutsuwa, muka daga taron sai yau Talata"

Taron dai, taro ne na neman hadin kan jihohin da gwamnonin PDP bakwai da ke yi wa uwar jamiyyarsu tawaye, don su shiga jamiyyar APC a yi tafiya tare a siyasar 2015.

Bayan dai gabatar da jawabi cikin turanci da shugaban tawagar ta jamiyyar APC, wato janar Muhammadu Buhari ya yi, inda ya nemi da jama'ar jihar Rivers su shigo a yi tafiya tare, Janar din ya kara wa wakilinmu Muhammad Bello bayani, kan zabubbukan kasar

Buhari ya ce "babban abin shi ne a tabbatar an yi zabe kan ka'ida don duk abinda muke yi bazaar bari ayi zaben ba zuwa za ai a rubuta,aje gidan rediyo a fadi,ace in mutum yana da magana ya tafi wurin shari'a to abin ba zai yi wu ba. Sabo da haka wannan ya danganta ga 'yan Najeriya, dukkansu su tabbatar sun zabi wadanda su ke so su wakilce su, su kuma shugabance su"

Da yake maida jawabi a maimakon jamaar jihar Rivers, Gwamna Rotimi Amaechi, ya fara da yin jawabin na hannunka mai sanda , inda yace.

Senator Lawali Shuaibu, General secretary ANC party. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa aus Abuja in Nigeria

Lawali Shuaibu, jigo a jam'iyyar APC

"Kamata ya yi mutum ya san cewar in har ka yarda da Uban giji, to babu kuma shayin wani. Kuma an sha za a cire ni daga gwamna, tun shekara ta 2007, amma har yau ina nan daram"

Daga karshe dai Gwamna Amaechi ya nunar cewar ya ji gayyatar ta jamiyyar APC, kuma za a yi shawara da jama'ar Rivers da kuma gwamnoni bakwai na Kasar, Kafin yanke hukunci.

©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace

Shugaba Goodluck Jonathan

Wannan taro dai da aka yi kusan kukan kurciya ne, tare kuma da fitowa karara don yin adawa da fadar gwamnatin Najeriya, a daya daga zuciyar jihohin yankin Niger Delta, inda shugaba Goodluck Jonathan ya fito. Masu sharhin siyasa na hangen cewar, labudda akwai kallo ga mai yawan rai a siyasar 2015, bisa la'akari da yadda adawa ke dada ruruwa daga yankin shugaban kasar.

Mawallafi: Muhammad Bello

Edita: Usman Shehu Usman