Shugabanni na son sabuwar makoma ga duniya
September 25, 2015Talla
Shugabannin kasashen duniya a wannan Jumma'a a birnin New York na Amirka a taron kolinsu zai amince da shirin kakkabe bakin talauci da yaki da sauyin yanayi da ma wasu batutuwa da ke zama kalubale a tsakanin kasashen duniya, karkashin wani tsari da zai lakume makuden kudade cikin burin da suke da shi a tsawon shekaru 15 masu zuwa.
Wannan sabon shirin samar da sauyi na ci gaba, ana sa ran za a kashe tsakanin Dalar Amirka Tiriliyan uku da rabi zuwa tiriliyan 5 a kowace shekara har zuwa 2030.
Shugabannin da ake sa ran jawabansu a yayin taron kolin sun hada da Shugaba Barack Obama na Amirka da Xi Jinping na China da kuma shugabannin kasashen Masar da Iran da Indiya da Jamus da Birtaniya da kuma Faransa.