Shugaban ′yan sanda na Ferguson ya yi marabus | Labarai | DW | 12.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban 'yan sanda na Ferguson ya yi marabus

Thomas Jackson ya ajiye aiki bayan binciken da ofishin ministan shari'a ya gudanar cewar 'yan sandar a Ferguson suna cin zarafin baƙar fata.

Shugaban 'yan sanda na Ferguson da ke cikin jihar Missouri a Amirka ya yi marabus.inda kwanan baya a garin da ke cikin jihar Missouri jama'a suka yi ta yin bore.

Bayan kisan wani matashi baƙar fata Michael Brown da wani ɗan sandar farar fata ya yi a cikin watan Agustan da ya gabata. wannan marabus na Thomas Jackson ya zo ne bayan wani sakamakon bincike da ofishin minista shari' a na Amirka ya bayyana kan cewar 'yan sandar na cin zarafin baƙar fata a Amirka.