Shugaban Turkeministan Saparmurat Niyazov ya rasu sakamakon ciwon zuciya
December 21, 2006Talla
Sa´o´i kalilan bayan mutuwar ba zata ta shugaban Turkmenistan Saparmurat Niyazov, an nada mukaddashin sa Gurbanguly Berdy-Mukhammedov a matsayin shugaban wucin gadi. Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarun kasar ya bayar ta rawaito majalisar tsaro na cewa za´a bude wata shari´a ta masu laifi akan shugaban rikon, wanda ya kamata da ya maye gurbin tsohon shugaban kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. A karshen wani taron hadin guiwa, majalisar dokoki da ta tsaro sun ki su bayyana sunan sabon shugaba saboda shari´ar da ake jiran yi wa shugaban rikon. Da sanyin safiyar yau shugaba Niyazov dan mulkin kama karya, ya rasu ya na da shekaru 66 sakamakon ciwon zuciya.