Shugaban Tunisiya zai janye jam′iyyarsa daga cikin kawancen gwamnati | Labarai | DW | 11.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Tunisiya zai janye jam'iyyarsa daga cikin kawancen gwamnati

Bayan shafe kwanaki cikin rudanin siyasa, Shugaban Tunisiya Monsef Marzouki ya bayyana shirin janye jam'iyyarsa daga cikin kawance gwamnati

Bayan shafe kwanaki cikin rudanin siyasa, Shugaban Tunisiya Monsef Marzouki ya bayyana shirin janye jam'iyyarsa daga cikin kawance gwamnati mai ra'ayin Islama.

A cikin wata sanarwar kakakin jam'iyyar ta Congress for the Republic Party, ya ce, bukatar su ta neman maye gurbin ministoci biyu masu ra'ayin Islama bai samu ba.

A wannan Litinin ake saran tabbatar da matsayin. Jam'iyyar Ennahda mai ra'ayin Islama wadda ke mulkin kasar ta Tunisiya, ta shiga cikin mawuyacin hali, tun bayan kisan jagoran 'yan adawan kasar Chokri Belaid cikin makon jiya, abun da ya janyo zanga zanga da kuma kai ruwan rana tsakanin jami'an tsaro da tunzirin mutanen da su ka fusata.

Firaministan kasar Hamadi Jebali ya bayyana shirin kafa gwamnatin kwararru domin rage zaman tankiya, amma akwai turjiya daga jam'iyyar Ennahda mai mulki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas