1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kais Saied ya kara wa kansa iko

Abdul-raheem Hassan
February 13, 2022

Matakin na Shugaba Saied ya zo ne mako guda bayan da ya ce zai rusa majalisar koli ta shari’a, lamarin da ya sa alkalan kasar suka rufe kotuna kasar kan zargin keta ‘yancin shari’a.

https://p.dw.com/p/46x6r
Tuniya | Zanga-zanga
Hoto: Yassine Gaidi /AA/picture alliance

Daruruwan masu zanga-zanga sun yi tattaki a tsakiyar birnin Tunis don bayyana fargaba na samun hukumar shari'a mai cin gashin kanta. Yanzu dai Shugaban Tunisiya Kais Saied ya maye gurbin wata babbar hukumar shari'a da ya ba shi karfin ikon korar alkalan kasar, tare da hana su shiga yajin aikin.

Dokar kafa sabuwar majalisar kolin shari'a ta wucin gadi da shugaban kasar ya nada, ta ba shi ikon korar duk wani alkali da ya kasa yin aikin sa na kwarewa. Haka kuma dokar ta hana alkalai na kowane matsayi shiga yajin aiki ko gudanar da duk wani shiri na hadin gwiwa da zai kawo cikas ko jinkirta ayyukan shari'a kamar yadda aka saba.

Ko watan Yulin 2021, Shugaba Saied ya rusa gwamnatin kasar ya kuma dakatar da majalisar dokokin tare da kwace madafun iko da dama kafin ya karawa kansa karfin ikon mulki, lamarin da ya haifar da fargabar rushewar dimokuradiyya.