Shugaban Somalia ya shiga Mogadishu | Labarai | DW | 09.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Somalia ya shiga Mogadishu

Shugaban kasar Somalia Abdullahi Yusuf ya shiga babban birnin kasar Mogadishu karo na farko tun lokacinda ya kama aiki a matsayin shugaban kasar a 2004.

Wannan kuwa ya zo ne bayanda dakarun gwamnati tare da goyon bayan dakarun kasar Habasha sun kori magoya bayan kotunan islama ne daga birnin.

Kafin isarasa babban birnin kasar ta Somalia,shugaba Yusuf ya soke batun tattanawara zaman lafiya da magoya bayan kotunan na islama.