1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Senegal ya amince da dokar hukunta auren jinsi

Abdoulaye Mamane Amadou
March 31, 2026

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya rattaba hannun kan dokar hukunta masu aren jinsi da majalisar dokokin kasar ta amince da ita a farkon wannan wata.

https://p.dw.com/p/5BSPR
Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye
Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye FayeHoto: Light Oriye Tamunotonye/AFP

Shugaba Bassirou Diamaye Faye na kasar Senegal ya sanya hannu kan dokar haramta auren jinsi da majalisar dokokin kasar ta kadawa kuri'a a ranar 11 ga watan Maris na wannan shekara, dokar ta tanadi hukunci ga duk wanda ya tallata ko ya bayar da taimakon kudaden da suka shafi masu auren jinsi a kasar Senegal.

Senegal ta bukaci a ninka hukuncin aikata auren jinsi

Babban jami'in kare hakkin dan'Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi Allah-wadai da dokar yana mai cewa ta sha bam-ban da mutunta hakin dan'Adam, inda sabuwar dokar ta kuma tanadi tarar kudi daga miliyan biyu zuwa miliyan 10 na kudin CFA, sabanin tarar da ta kasance a baya.

Shekaru biyu da haramta auren jinsi a Yuganda

Mafi yawan 'yan kasar Senegal Musulmi ne, sannan sun jima suna cece-kuce kan batun dokar wacce ta tayar da kura tun bayan kama wasu mutum 12, ciki har da fitattun ‘yan wasa biyu a farkon watan Fabrairun wannan shekara.