Shugaban Kwalambiya ya lashe kyautar Nobel ta bana | Labarai | DW | 07.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Kwalambiya ya lashe kyautar Nobel ta bana

Duk da gaza cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin kasar Kwalambiya da kuma kungiyar FARC ta 'yan tawayen kasar, shugaban kasar ta Kwalambiya Juan Manuel Santos ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta bana.

Shugaban kasar Kwalambiya Juan Manuel Santos ya samu nasarar lashe kyautar wanzar da zaman lafiya ta Nobel ta bana. Kokarin da Manuel Santos ya yi na kawo karshen yakin da kasarsa ke fama da shi na tsahon sama da shekaru 50 ne dai ya bashi damar lashe wannan kyauta da ake bai wa mutanen da suka shaharaa wajen kawo zaman lafiya. Koda yake kokarinsa na tabbatar da sulhun ya samau nakasu bayan da kuri'ar raba gardamar kan tabbatar sulhun da al'ummar kasar suka kada ta yi watsi da batun zaman lafiyar tsakanin gwamnati da 'yan tawayen kasar na FARC, amma hakan bai hana a baiawa Santos wannan kyauta ba. Akwai dai fargabar cewar gaza cimma yarjejeniyar sulhun da 'yan tawayne na FARC na kasar Kwalambiya, ka iya haifar da barkewar wani sabon yakin basasa a kasar.