Shugaban Indonesiya ya sanar da abokin takararsa
August 9, 2018Talla
Shugaba Joko Widodo ya ce Ma'ruf Amin mai shekaru 75 da haihuwa wayayyen malamin addinin Islama ne, sannan dukkanin jam'iyyu tara da suka yi hadaka sun amince da zabin nasa. A ranar Juma'a shugaba Widodo da Amin za su yi rijista a hukumar zaben kasar.
Kasar Indonesiya wacce ta kasance daya daga cikin kasashen duniya masu yawan Musulmi za ta gudanar da zabe a watan Afrilun shekara ta 2019.
Har yanzu dai babu wani raddi game da batun zabo Ma'ruf Amin daga bangaren mataimakin shugaban kasar Muhammad Yussuf Kalla, wanda ya kasance mutum na farko a kasar da ya yi mataimakin shugaban kasa sau biyu.