Shugaban kasar Bama ya yi murabus
March 21, 2018Babu dai wani bayani da shugaban ya bayar a game da dalillansa na yin murabus din, sai dai kafofin yada labaran kasar da dama sun danganta matakin da tarbarbarewar yanayin lafiyar jikin shugaban.
A watan Aprilun shekara ta 2016 ne Shugaban wanda ke daya daga cikin abokanan gwagwarmayar Aung San Suu Kyi a shekarun baya, ya karbi ragamar mulkin kasar ta Myanmar ko Bama inda ya zamo shugaban farar hula na farko a cikin gwamman shekaru na baya-bayan nan na tarihin kasar. Sanarwar fadar shugaban kasar ta bayyana cewa za a nada sabon shugaban kasa a cikin mako daya daga yanzu.
Majalisar Dinkin Duniya dai na zargin gwamnatin kasar ta Bama da aikata kisan kiyashi kan al'ummar tsirarun Musulmin kasar 'yan kabilar Rahongyas wadanda yanzu haka sama da dubu 70 suka tsere zuwa makobciyar kasarsu ta kasar Bangladesh domin tsira da rayukansu daga kisan da suke fuskanta a kasar.