Shugaba Afwerki na Iritiriya ya isa Habasha
July 14, 2018Talla
Shugaba Isaias Afwerki ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai kasar ta Habasha, inda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku. Shugaban ya ce a halin da ake ciki kasashen biyu sun zama 'yan uwan juna don haka batun zaman 'yan marina tsakaninsu ya zama tarihi.
A nasa jawabin, mai masaukin baki Firaministan Habasha Abiy Ahmed jinjinawa hukumomin Iritiriya ya yi musamman ma shugaban kasar kan amincewa da shirin wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, inda ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru wajen dorewar sabon kawance da bangarorin biyu suka kulla.