Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga al’ummansa da ke hamayya da juna da su tsagaita buɗe wuta tsakaninsu. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga al’ummansa da ke hamayya da juna da su tsagaita buɗe wuta tsakaninsu.

Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya yi kira ga dukkan al’ummansa da magoya bayan ƙungiyoyin Fatah da Hamas da su sulhunta rikicin da ke tsakaninsu ta hannunka mai sanda, sa’annan su fi Mai da hankalinsu wajen daddage wa matakan da Isra’ila ke ɗauka na gina katanga da kuma matusugunai a harabobin gaɓar Yamma.

Mahmoud Abbas, ya yi wannan kiran ne a wani taron jam’iyyun Falasɗinawan da aka kira don kwantad da ƙurar rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan jam’iyyarsa Fatah da na ƙungiyar Hamas, masu jan ragamar Hukumar Falasdinawan a halin yanzu. Amma ya kuma yi barazanar kiran zaɓen raba gardama, idan ɓangarorin biyu ba su yarje kan wasu shawarwarin da shugabannin Falasɗinawan da ke ɗaure a kurkuku a halin yanzu suka gabatar, na kawo ƙarshen rikicin ba. Mahmoud Abbas dai ya bai wa taron wa’adin kwana 10 ne da ya cim ma yarjejeniya.