Shugaban ECOWAS na ziyara Mali | Labarai | DW | 11.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban ECOWAS na ziyara Mali

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da ke jagorantar kungiyar ECOWAS ya sauka Bamako kasar Mali a karon farko bayan dage wa Mali takunkumi sakamakon juyin mulki.

Shugaban ECOWAS ya samu tarabar shuzgaban rikon kwarya  Bah N'daw a filin jirgi, kana ya kuma gana da mataimakin shugaban kasar Assimi Goita wanda ya jagoranci kifar da gwamnatrin tsohon shugaban Ibrahim Boukar Keita a watan Agusta.

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin aksashen Afirka ECOWAS ko CEDEAO sun dage takunkumi karya tattalin arzikin Mali bayan da sojiojin da suka kifar da mulkin suka amince da maida kasar karkashin mulkin farar hula zuwa lokacin shirya sabon zabe, tare da yarjejeniyar sake wadanda aka kama loakcin juyin mulkin.