Shugaban Chaina da na Taiwan sun gana | Labarai | DW | 07.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Chaina da na Taiwan sun gana

Ganawar da ta gudana a kasar Singapour na a matsayin ta farko a cikin shekaru 66 na bayan bayan nan tsakanin wani shugaban kasar Chaina da na Taiwan masu gaba da juna

Shugabannin kasashen Chaina da Taiwan sun yi wata ganawa mai cike da tarihi a wannan Asabar a kasar Singapor. Ganawar wacce ita ce irinta ta farko da ta taba hada wasu shugabannin wadannan kasashe biyu a cikin shekaru 66 na baya bayan nan ta kasance mai cike da shauki.

A lokacin haduwar tasu Shugabannin biyu Xi-Jinping na Chaina da takwaransa Ma Yin-Jeou na Taiwan sun rike hannun juna na tsawon sama da minti daya suna masu yiwa juna murmushi a gaban tarin 'yan jarida a dakin taro na wani Hotel na kasar Singapor.

Daga ya ke jawabin a gaban takwaransa na Taiwan Shugaba XI na Chaina ya bayyana cewa wannan ganawa ta nunar da cewa babu wani abin da ka iya raba al'ummomin kasashen biyu.

Babu dai alamar an samun matsaya a lokacin ganawar amma ta kasance tamkar wani tsanin farko na neman mayar da hulda tsakanin kasashen biyu wadanda har kawo yanzu babu daya da ta amince da halaccin zaman 'yar uwarta