Shugaban Azerbaidjan ya da umarnin gudanar da binciken kisan mai sukarsa | Labarai | DW | 13.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Azerbaidjan ya da umarnin gudanar da binciken kisan mai sukarsa

Shugaban kasar Azerbaidjan Nursultan Nazarbayev ya ba da umarnin gudanar da bincike dangane da kisan gillar da aka yiwa mai sukar lamirin shugaban wato Zamanbek Nurkadilov. Kamar yadda lauyan iyalin sa ya nunar sun ga gawar mai adawa da gwamnatin ne a cikin gidansa kuma an harbe sau uku. Matarsa ce ta gano tsohon ministan wanda a da suke dasawa da shugaba Nazarbayev kwance jina jina fuskarsa na kasa. An harbe shi sau biyu a kirji sannan daya a ka inji lauyan. Shugabannin ´yan adawa sun ce kisan ba zai rasa alaka da sukar da Nurkadilov din ke yiwa shugaba Nazarbayev ba da kuma goyon bayan da yake nunawa ´yan adawa. To amma shugaban ´yan sanda ya musanta wannan zargi.