1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka Ta Tsakiya ya ce zai kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa

December 30, 2012

Francois Bozizé ya ce a shirye ya ke ya tattauna da ya tawayen ba tare da wasu sharuɗa ba, sannan ya ce ba zai sake tsayawa takara ba a zaɓen shugaban ƙasa

https://p.dw.com/p/17BQK
François Bozizé, Präsident von Zentralafrika. Central African Republic President Francois Bozize listens during a session on the 17th African Union Summit with theme of youth empowerment, at the Sipopo Conference Center, outside Malabo, Equatorial Guinea, Thursday, June 30, 2011. (AP Photo/Rebecca Blackwell)
Hoto: AP

Shugaban ƙungiyar Tarrayar Afirka kana kuma shugaban ƙasar jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi wanda ya gana da shugaban Afirka Ta tsakiya wannan Lahadin (30.12.12) a birnin Bangui, ya sanar da cewar shugaba Francoi Bouzizé ya yi alƙawarin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa domin saka 'yan tawaye a cikin gwamnatin.

Bayan tattaunawar da gwamnatin za ta yi da ƙungiyar yan tawayen Seleka a cikin sabon wata mai kamawa a birnin Librevile, na Gabon, shugaban kuma ya yi alƙawari ba zai sake tsayawa takara ba a zaɓen shugaban ƙasar na shekara ta 2012.Tun da farko yan tawayen waɗanda ke daf da birnin Bangui, fadar gwamnatin ƙasar sun ce buƙatar su ita ce a mutunta yarjejeniyar da aka cimma tsakaninsu da gwamnatin a shekara ta 2007. To amma daga bisani sun ce tilas ne shugaban ya sauka daga mulki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh