Shugaban Afirka ta Kudu zai bayyana a gaban majalisa | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaban Afirka ta Kudu zai bayyana a gaban majalisa

Shugaba Jacob Zuma, zai yi jawabinsa na shekara-shekara a gaban majalisar dokokin kasar, a daidai lokacin da ya ke fuskantar matsin lamba daga 'yan adawa.

Jacob Zuma

Jacob Zuma

'Yan adawar kasar ta Afirka ta kudu dai, na nema da Shugaban Zuma ya yi murabus sakamakon badakalar da ta taso kan batun gina wani katafaran gidansa mai na Nkandla da kudadan al'ummar kasar. Baya ma ga wannan batu, akwai kuma batun matsalar tattalin arzikin kasar wanda ake ci gaba da gani bayan korar ministocin kudin kasar har guda biyu da shugaban ya yi a watan Disamba da ya gabata.

Tuni dai jam'iyyar adawa ta EFF ta Julius Malema, ta sha alwashin tada tarzoma ya yin jawabin na shugaba Zuma muddin dai shugaban bai ba su haske ba kan batun korar mistocin kudin da ya haddasa faduwar darajar kudin kasar.