Shugaba Zuma na kara shan matsin lamba | Siyasa | DW | 31.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shugaba Zuma na kara shan matsin lamba

Babbar kotun Afirka ta Kudu ta umarci Jacob Zuma da ya maida kudade da ya yi amfani da su wajen inganta gidansa ba bisa ka'ida ba.

Kotun kundin tsarin mulkin da ke zama babbar kotun koli dai ta karkare zamanta a wannan Alhamis da umartan shugaban kasa Jacob Zuma, da ya mayar da makudan kudaden da ake zarginsa da karkatasu wajen gyaran gidansa da ke Nkandla. Babban alkalin kotun kolin Afirka ta Kudun mai shari'a Mogoeng Mogoeng, ya ce wajibi ne da a zurfafa bincike kan yadda aka sarrafa wadannan kudade da ake alakanta su da samar da tsaro a gidan na shugaba Jacob Zuma.

"Akwai bukatar hukumar tara kudaden shiga ta kasar Afirka ta Kudu ta gudanar da bincike mai zurfi kan hakikanin kudaden da aka kashe wajen kwaskwarimar gidan shugaba Jacob Zuma da ke Nkandla, wanda baya da nasaba da tsaro kamar yadda yake ikirari."

Barazanar tsige shugaban kasa

A yanzu dai, shugaba Zuma, na cikin tsaka mai wuya, ganin tuni 'yan adawa suka fara barazanar tsige shi daga kan karagar mulkin kasar.

Südafrika Proteste gegen Jacob Zuma Staatspräsident

Masu boren neman Zuma ya maida kudin kasa

Babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ita ce kan gaba da ke ganin lokaci yayi da shugaban zai fuskanci fushin 'yan kasar da irin abin da suka kira cin amana ta karkata asusun gwamnatin kasa. Mmusi Maimane shi ne shugaban jam'iyyar ta Democratic Alliance.

"Abin mamaki shi ne a baiyane yake karara cewar, shugaba Zuma ya taka dokar kundin tsarin mulkin kasar Afirka ta Kudu. Sannan ya nuna cewa ya gaza kare kalamansa na kare dukiyar kasa da martaba doka a lokacin da yayi rantsuwar kama aiki. Da wadannan hujjoji muke cewa yanzu ya zama wajibi shugaba Jacob Zuma ya bar kujerar shugabancin kasar."

To sai dai kawo yanzu, jam'iyyar African National Congress da ke mulkin kasar, ta ce za ta yi nazarin hukuncin kotun, na yiwuwar biyan kudaden da ta umarci shugaba Zuman ya biya ko a'a. Shugaba Zuma dai ya ce zai mutunta hukuncin kotun.

Demokradiyya da mulkin doka sun girku

Südafrika Proteste gegen Jacob Zuma Staatspräsident

Zuma na shan suka daga bangarori da dama na kasa

'Yan kasar Afirka ta kudun dai, na wa kallon matakin da kotun ta yanke a matsayin alamar karfafa demokradiyya kamar yadda wani dan kasar ke bayyana ra'ayinsa.

"Na yi farin cikin ganin kasarmu ta dau hanyar dabbaka tsarin demokradiyya, yanzu dai ko wane dan Afirka ta Kudu ya tabbatar da cewa muna kan turba madaidaiciya kamar tsarin 'yan Adam da ke bin tsarin dokoki. Mu sani cewa babu wanda ya fi karfin doka."

A yanzu dai babbar kotun ta kaiyade kwanaki 105 ga shugaban Zuma da ya biya kudaden zuwa asusun baital-malin kasar Afirka ta Kudun. An dai yi amfani da kudi dala miliyan 17 ne don aikin kwaskwarimar gidan shugaba Jacob Zuma, inda aka tanadi makeken tafkin wanka da ninkaya irin na zamani da babban filin taro. Kana an kebe wurin garken shanu na musamman a cikin gidan duk dai da sunan sarrafa gidan da tsarin samar da tsaro ga shugaban.

Sauti da bidiyo akan labarin