Shugaba Zuma na fuskantar matsin lamba | Labarai | DW | 05.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Zuma na fuskantar matsin lamba

Jiga-jigan jam'iyar ANC mai mulkin Afirka ta Kudu na ganawar gaggawa kan daukar mataki na gaba kan yunkurin Shugaba Jocob Zuma na yin watsi da bukatar yin murabus.

Shugabannin jam'iyar ANC za su nazarci shugabancin jam'iyar, tare da daukar matakai kan kudirin jam'iyun adawa da ke shirin kada kuri'ar yanke kauna kan shugaban Zuma a ranar 22 ga watan Fabrairu.

Gabannin wannan taro dai sai da aka samu jerin zanga-zanga daga bangaren masu Allah sambarka da 'yan Allah wadai da shugabancin shuga Zuma. Inda wasu kusoshin jam'iyar ANC na fatan ganin sabon shugaban jam'iyar Cyril Ramaphosa ya gaji shugaba Zuma, yunkurin da ke fuskantar tirjiya daga magoya bayan shugaba Zuma.

A yanzu dai ANC na da burin shawo kan mastalar da ke addabar jam'iyar, domin kare martaba da tasirinta a babban zaben kasar da ke tafe.