1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Trump ya gargadi jam'iyyar Demokrat bayan zabe

Ramatu Garba Baba
November 7, 2018

A jawabinsa bayan fitar da sakamakon zaben rabin wa'adi, shugaban Amirka Donald Trump ya ce duk da rashin rinjaye a majalisar wakilai wannan ba hujja ba ce ga jam'iyyar Demokrat na son yi wa gwamnatinsa bita da kulli.

https://p.dw.com/p/37qxY
USA, Washington:  Präsident Trump bei einer Midterm elections Pressekonferenz im Weißen Haus
Hoto: REUTERS

Trump ya gargadi 'yan jam'iyyar Demokrat da suka lashe akasarin kujerun 'yan majalisar wakilai da kada su nemi yin amfani da nasarar don soma tuhumarsa, batun da ya ce ba zai lamunta muddun suka nemi yin almubuzurranci da dukiyar kasa wajen gudanar da bincike.

Baya ga wannan, shugaban ya kuma ce zai cigaba da yin kokari wajen ganin majalisa ta amince da bukatarsa ta sakin kudi don gina katanga tsakanin Amirka da Mexiko inda a share guda ya nemi hadin kai a ayyuka da suka shafi fannin lafiya da gina kasa.

Zaben rabin wa'adi da aka gudanar a jiya Talata ya kara nunawa karara yadda da dama daga cikin Amurkawa ke goyon bayan shugaban duk da tarin zanga-zangar da aka gudanar tun bayan da ya soma mulki shekaru biyu da suka gabata na nuna adawa da tsare-tsarensa.