1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: Zanga-zanga kan ziyarar Trump

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 13, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya samu rakiyar masu zanga-zangar adawa da ziyarar da ya ke a Birtaniya.

https://p.dw.com/p/31Pdt
Großbritannien Anti-Trump Proteste in London
Zanga-zangar adawa da ziyarar Trump a BirtaniyaHoto: Reuters/S. Dawson

Yayin wannan ziyara Firaministar Birtaniyan Theresa May da shugaban Amirka Donald Trump sun ziyarci makarantar horar da sojoji da ke Birtaniya a Sandhurst, kafin daga bisani su dawo fadar gwamnatin, inda May za ta yi wa Trump karin haske kan tsare-tsaren da take bi masu sassauci, na kammala ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Tuari EU. Tun da farko yayin hira da wata jarida, Trump ya ce in har May ta yi amfani da tsarin nata, dangantakar da ke tsakanin Birtaniya da Amirka ka iya zuwa karshe. May da Trump sun gana a wani wuri da ke gefen Ingila, inda daga bisani Trump zai kai ziyara ga sarauniyar Ingilan Elizabeth ta II.