Shugaba Sassou Nguesso na Kwango na neman sake takara | Labarai | DW | 23.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Sassou Nguesso na Kwango na neman sake takara

A wani jawabi ne da ya yi ta kafofin yada labarai, shugaban ya ce zai baiwa ail'ummar kasar damar fadar albarkacin bakinta kan batun sake tsayawarsa takara.

Denis Sassou-Nguesso

Denis Sassou-Nguesso

Shugaban kasar Kwango Brazzaville Denis Sassou Nguesso, ya sanar da aniyarsa ta kiran wani zaben raba gardama nan gaba a kasar, domin a cewarsa baiwa al'umma damar fadin matsayinta kan yuyuwar sake tsayawarsa takara a wani sabon wa'adin mulki. Shugaban da a halin yanzu ya shafe fiye da shekaru 30 a kan karagar mulkin kasar, ya yi wannan batu ne cikin wani jawabi da ya yi ta gidan radio da talbijin na kasar.

Shugaban kasar ya bullo da wannan batu ne, inda ya sanar da kafa wani kwamitin da zai yi nazarin sabon daftarin kundin tsarin mulkin da kuma kiran zaben raba gardama nan gaba ba da jimawa ba. Sai dai a cewar Clement Mierassa, daya daga cikin shugabannin jam'iyyun siyasa na bangaran adawa a kasar, wannan wani mataki ne da zai tsunduma kasar cikin wani rudani na siyasa.