Shugaba Obama da Castro sun yi musabaha
April 11, 2015A cewar Bernadette Meehan da ke magana da yawun cibiyar samar da tsaro a Amirka, shugabannin biyu sun hadu suka gaisa kafin bude taron kolin na kasashen Latin Amirka da ke gunadana a Panama .
Shugaban kasar ta Cuba Raul Castro da shugaba Barack Obama na Amirka, sun yi musabahar ne a jiya Juma'a karon farko da shugabannin kasashen biyu ke ganawa, tun bayan da aka shiga tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu a farkon shekarar 1961.
Wannan gayyata da aka yi wa kasar ta Cuba dai, na zama karon farko da aka yi mata dan halartar taron kasashen Latin na Amirka.
A cewar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, bayyanar ta shugaba Raul Castro a wajen taron wani abu ne da aka dade ana jimirin gani.
Shugaba Castro kafin ya zauna cikin jerin shugabanni a wajen taron, ya tafa da ma dan yin wasannin ban dariya da shugaba Juan Carlos na kasar ta Panama da mai dakinsa.