Shugaba Nkurunziza ya yi tayin yin afuwa | Labarai | DW | 02.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Nkurunziza ya yi tayin yin afuwa

Shugaba Nkurunziza ya yi tafin yin afuwa ga mutanen da za su mika makamansu daga cikin wadanda suka dauki makamai lokacin kokowa da shirinsa na tazarce

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya yi alkawarin yin afuwa ga duk wadanda za su mika makamansu daga cikin mutanen da suka dauki makamai a lokacin kokowa da shirinsa na tazarce. Shugaba Nkurunziza ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya gabatar wa 'yan kasa a cikin harshen Kirundi na kasar tasa a wannan Litanin ta gidajen radiyo da talabijin na gwamnatin kasar inda ya ce ya bai wa mutanen wa'adin kwanaki biyar daga yau Litanin domin mika makaman nasu.

Shirin yin afuwar na Shugaba Nkurunziza ya kuma tanadi bai wa mutanen da za su mika makaman nasu horo na tsawon mako biyu kan batun kishin kasarsu kana a maidasu gidajensu ba tare da wata tsangwama ba.

Haka zalika a jawabin nasa Shugaba Nkurunziza ya kuma yi kira ga al'ummar kasar tasa da su bai wa jami'an 'yan sandar kasar goyan baya wajen karya lagon kungiyoyin mutanen da ke aiwatar da kishe-kishen gilla a kasar.