Shugaba Mursi yayi jawabi ga ′yan kasar | Labarai | DW | 07.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Mursi yayi jawabi ga 'yan kasar

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban kasar ta Masar ya fito ya bayana matsayinsa a dangane da rikicin da ya barke a kasar.

default

Mohamed Mursi na Masar

A daren wannan Alhamis ne, shugaba Mohamed Mursi na Masar yayi wani jawabinsa ga 'yan kasar ta hanyar kafofin yadan labaran gwamnati. Mursi ya gayyaci masu adawa da matakin nasa na karawa kansa karfin iko gurin wata tautaunawa ta keke da keke a wannan Asabar domin samun sararin warware bakin zaren da ya kulle a kasar tun lokacin da ya gabatar da kudurin da ke kara mishi karfin iko makoni biyu da suka gabata.To saidai babban hadin gwiwar jam'iyu da kungiyoyin adawan kasar sun ce za su yi nazarin wannan tayin da shugaban kasar ya musu,to amman kamun nan sun kira wani gagarumin jerin gwano a yau bayan sallar Juma'a domin kara jadada martsayinsu a dangane da batun inji kakakin hadin gwiwar.Wannan gayatar da shugaban kasar ta zo ne a daidai lokacin da shugaba Obama na Amurka ya kira takwaran nasa na Masar da shi samo hanyar warware rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 10 tun bayan barkewarsa. To saidai shugaban bai bayana jinye matakin nasa ba.

Mawallafi: Issoufou mamane

Edita Saleh Umar Saleh