1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Merkel na ziyarar Gabas Ta Tsakiya

Abdullahi Tanko Bala
June 21, 2018

'Yan kasashen Jordan da Lebanon su ne suka fi yawa cikin yan gudun hijira a duniya. A yayin wannan ziyarar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tattauna da shugabannin kasashen kan samar da mafita.

https://p.dw.com/p/2zznY
Jordanien | Angele Merkel zu Besuch in Amman
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a JordanHoto: Getty Images/AFP/A. Abdo

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Gabas Ta Tsakiya inda za ta je kasashen Jordan da kuma Lebanon.

A yayin ziyarar Merkel za ta gana da sarki Abdallah na Jordan da kuma Firaministan Lebanon Rafik Hariri.

Tattaunawar ta su za ta mayar da hankali kan fannoni da suka hada da Ilmi da zuba jari da kuma batun 'yan gudun hijira.


Dubban daruruwan yan gudun hijirar Siriya ciki har da wadanda Jordan ta tsugunar sun yi kaura zuwa kasashen Turai musamman ma Jamus.

Batun 'yan gudun hijirar dai ya haifar da sabani a kawancen jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da takwararta ta CSU.


A ranar Lahadi mai zuwa shugabannin kasashen Turan za gudanar da taro domin tattauna mafita ga matsalolin yan gudun hijirar.